Ranar abinci ta duniya

Hakkin mallakar hoto Farming Simulator

Ranar 16 ga watan Oktoba ce ranar abinci ta Duniya. Kuma taken wannan shekarar shine noma na iyali, ciyar da duniya, kulawa da duniya

A cewar hukumar abinci da ayyukan gona ta Majalisar dinkin duniya, an zabi taken ne domin a daga martabar noman iyali da kuma kananan manoma

Kuma ranar zata maida hankali ne akan mahimmancin noman iyali wajen magance yunwa da talauci da samar da abinci da inganta rayuwa da kare muhalli da cigaba mai dorewa musamman a yankunan karkara

Sai dai wasu kananan manom a Nigeria sun koka da rashin isasshen taki da kuma magungunan kashe kwari.