Obama: Ana bukatar mataki mai karfi kan ebola

Amber Vinson Hakkin mallakar hoto APS
Image caption Amber Vinson

Shugaba Obama ya ce dole ne matakin da za'a dauka game da cutar Ebola a Amurka ya kasance mai karfi.

Yayinda yake magana bayan wata ganawa da ya yi tare da manyan jami'an fadar sa ta White House, Mr Obama ya ce kamata yayi tawaggar ma'aikatan kiwon lafiya na kasa su dauki mataki nan take, muddin aka sake samun bullar cutar cikin sa'oi 24.

Ya kuma ce yana da mahimmanci a taimakawa kasashen Afirka dake kokarin shawo kan annobar.

Mr Obama na magana be bayan da aka tabbatar da cewa wata ma'aikaciyar jinya a Texas ta kamu da kwayar cutar, bayan ta yi jinyar wani dan- kasar Liberia da ya mutu sakamakon kamuwa da cutar.

Hukumomin Amurka sun ce suna son su gudanar da gwaji akan dukkanin mutanen da suke cikin jirgin da ma'aikaciyar jinyar ta shiga