Ebola: An kaddamar da asusun neman taimako

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Karo na biyu ke nan da ake kaddamar da asusun neman taimakon yaki da cutar ebola

Babban sakataren Majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya kaddamar da wani asusun neman taimakon kudade na gaggawa domin taimakawa wajen yaki da cutar ebola

Ban Ki Moon ya ce an samu dala dubu dari ne kachal a asusun dala biliyan gudar daya kaddamar a watan Satumba.

Wadanda suka bayar-da gudummuwar kudaden sun bada kusan dala miliyan dari hudu ne ga wasu hukumomin Majalisar dinkin duniyar da kuma kungiyoyin bayarda agaji.

Amma assusn kansa ya samu alkawuran dala miliyan ashirin ne kawai, kuma ya zuwa yanzu kasar Colombia ce kadai ta bayar da gudummuwarta