Apple ya kaddamar da iPad Air 2 da iPad Mini 3

Hakkin mallakar hoto PA

Kamfanin Apple ya bada sanarwar kirkiro da iPad Air 2 wacce ya ce ita ce mafi siranta da ya taba fitowa da ita a kasuwa

Tana da kaurin 6.1mm kuma tana iya gane dan- yatsan mutumin da ya taba ta.

Tana da wata kariya a fuskarta a karo na farko

Sai dai wasu masu sharhi na tababar ko yadda aka inganta ta, ka iya yin tasiri a kasuwar saida iPad.

Apple ya kuma bada sanarwar kirkiro da iPad Mini 3.

Apple ya bayyana cewa ya saida iPad guda sama da miliyan 13 a watan Afrilu zuwa Yuni.

Sai dai ya samu komabaya da kashi 9% ke nan idan aka kwatanta da shekarar 2013 duk kuwa da cewa kasuwar kamfanin ta iPhone da kuma Mac computers din da ya sayar ta karu.