Ebola: Hukumar Lafiyar Duniya ta tashi tsaye

Ebola Hakkin mallakar hoto Getty

Kungiyar lafiya ta duniya ta ce tana mayar da hankali a kan karin kasashen Afrika goma sha biyar a kokarinta na hana yaduwar cutar Ebola.

Ta ce an zabe su ne saboda suna da kan iyaka daya tare da kasashe 3n da cutar ta fi shafa -- Liberia da Saliyo da kuma Guinea -- ko kuma suna da muhimmiyar alakar cinikayya da ta sufuri.

A Saliyo, an tabbatar da kamuwar wani mutum da cutar a gunduma dayar da ta rage ba a samu bullar cutar ta Ebola a cikinta ba -- don haka a halin yanzu cutar ta game daukacin kasar.

Alhassan Kemokai yana daya daga cikin wadanda suka warke daga cutar ta Ebola a Saliyo din, ya ce wadanda suka warke daga cutar nada rawar da za su taka wajen ilmantar da saura:

Ya ce, “Ga duk wanda ya haye daga wannan cuta, hakkinka ne ka kuma fadakar da al'umarka, ka kuma fadakar da wanda cutar ba ta kama ba ta yadda za su yi hattara, kar su kamu da cutar.”