2015: "Jonathan zai tsaya takara"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jonathan zai bayyana aniyarsa nan gaba kadan

Mai bai wa shugaban Nigeria Goodluck Jonathan shawara na musamman ya ce nan gaba kadan ne shugaban zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben shekarar 2015.

Dr Doyin Okoupe ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa 'yan kasar da dama suna ta yin kira ga shugaba Jonathan ya tsaya takara domin ya ci gaba da ayyukan da yake yi.

Ya kara da cewa zargin da Janar Muhammadu Buhari ya yi cewa shugaban bai tsinana komai ba ba gaskiya ba ne.

Ranar Laraba ne dai tsohon shugaban na Nigeria, Janar Buhari, ya zargi shugaba Jonathan da daurewa cin hacin da rashawa gindi, da sanya 'yan kasar cikin mummunan talaunci da gaza hana kasashe-kashe.

Janar din ya kuma bukaci 'yan kasar su zabe shi a shekarar 2015 domin ya magance musu wadannan matsaloli.

Karin bayani