An yanke wa jami'in China hukuncin kisa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kasafin kudin ma'aikatar jiragen kasa na China na da matukar yawa

Kafar watsa labaran gwamnatin China ta ce an yanke wa wani injiniyan jirgin kasa hukuncin kisa bayan an kama shi da laifin karbar cin hancin kusan dala miliyan takwas.

Hukuncin da aka yi wa Zhang Shuguang na zuwa ne fiye da shekara daya bayan an yanke irin wannan hukunci kan tsohon ministan safarar jiragen kasa na kasar, Liu Zhijun.

Mutanen biyu dai su ne suka yi ruwa-da-tsaki wajen bunkasa layukan jiragen kasa masu matukar sauri a kasar.

Masu aiko da rahotanni sun ce mutanen biyu sun yi dumu-dumu a cin hanci da rashawa kasancewa kasafin ma'aikatar na da matukar yawa.

Karin bayani