Rikici ya sake barkewa a Hong Kong

Hakkin mallakar hoto
Image caption Masu zanga zanga na cewa basu yadda China ta ce ga wanda zai tsaya zabe a Hong Kong ba

Masu zanga zanga a Hongkong sun sake mamaye tituna a lardin Mongkong bayan da hukumomi suka tarwatsa su.

'Yan sanda sun yi artabu da dalibai a lardin Mong Kok, yayinda masu fafutuka dubu Tara suka sake fitowa domin sake karkafa shingayensu.

''Yan sandan sunce an jikkata jami'ansu 15, sannan an tsare mutane 26

Masu zanga zangar na son cikakken tsarin demokradiya a Hong Kong, sai dai Beijing ta hakikance da cewa tana da ta cewa a zabar wanda zai tsaya zabubukan da za'a yi a 2017