APC ta yi watsi da batun tsagaita wuta

Jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria ta ce ba zata amince da sanarwar yarjejeniyar tsagaita wutar da gwamnatin Nigeria ta yi shelar ta kulla da mayakan Boko Haram ba, har sai ta gani a kasa.

Jam'iyyar ta yi zargin cewa wannan ba shi ne karo na farko da gwamnatin Nigeriar take wannan ikirari ba, daga baya kuma tace sai 'yan kungiyar su cigaba da kai hare harensu.

A ranar jumu'a ne dai gwamnatin Nigeriar ta bada sanarwar yarjejeniyar tsagaita wutar da kungiyar Boko Haram.

Sai dai har yanzu kungiyar ba tace komai ba game da wannan batu.

Kwana guda kuma bayan sanarwar yarjejeniyar, wasu da ake zargin 'yan Kungiyar Boko Haram ne sun kai hare hare a wasu garuruwa a jahar Borno da kuma Adamawa.