An kashe mutane da dama a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP

A jihar Borno wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hare-hare ne a garuruwan Abadam da Dzur a ranakun Juma'a da Asabar.

Hare haren dai na zuwa ne bayan da gwamnatin Nigeriar ta yi shelar tsagaita wta da 'yan kungiyar Boko Haram.

A jihar Adamawa kuwa an kai harin ne ranar Asabar a kauyen Pina da ke cikin karamar hukumar Michika.

A wani hari, ance 'yan bindigar sun kashe manyan mutane da- dama a kauyen Abadam dake arewacin jahar ta Borno, da kuma tilastawa mutane da dama tserewa zuwa Niger mai makwabtaka da Nigeriar.

Sai dai hukumomin Nigeriar na cewa maiyiwuwa wasu gungun masu laifi ne suka kaddamar da hare haren akan kauyukan Bornon guda biyar.

Karin bayani