An samu rabuwar kawuna a fadar vatican

Hakkin mallakar hoto AP

Kungiyoyin kare hakkin 'yan luwadi sun bayyana rashin jin dadinsu game da yadda bishop- bishop suka yi watsi da wasu sauye- sauye da suka shafi 'yan luwadin da masu madigo da kuma ma'auratan da suka rabu

Paparoma Francis ya samu koma baya a yunkurin sa na sauya matsayin cocin Roman Catolika akan 'yan luwadin da kuma ma'auratan da suka rabu dama wadanda sukai aure a kotu.

A karshen taron manyan Limaman cocin na makonni biyu, fadar Vatican din ta gaza samun kashi biyu- bisa- uku na bishop- bishop da zasu mara mata baya akan wadannan batutuwa.

Daftarin farkon dai ya yi kira ne da a rungumi 'yan luwadin da kuma amincewa da dukkanin ma'auratan da suka rabu da wadanda sukai aure a kotu