Burtaniya na ba China shawara kan gina birane

China
Image caption Burtaniya za ta taimaki China wajen tsarin gina sabbin birane domin kaucewa yin illa ga muhalli.

Kwararru daga Burtaniya za su baiwa kasar China shawara kan yadda za ta gina birane ba tare da haifar da wata illa ga muhalli ba.

Ana sa ran kwararrun za su gana da magadan garin kasar domin a lalubo hanyar da za a kaucewa irin tsarin gine-gine na birnin Los Angeles dake da cunkoso a Amurka.

Burin da ake so a cimma shine samar da tsari a fannin sufuri da kuma gine-ginen da za su ba da damar samun iska.

Wannan ziyara ta biyo bayan wani rahoto da ya yi gargadin cewa bin tsarin yanayin gine-ginen kasar Amurka zai iya kawo cikas ga yakin da ake yi da matsalar dumamar yanayi.

Wani rahoton wanda hukumar Global Commission mai kula da tattalin arziki da muhalli ta fitar ya nuni da cewa nan da shekaru masu zuwa mutane biliyan biyu za su yi kaura zuwa birane a sassa daban daban na duniya.

A cewar rahoton, da karin kudi kadan, za a iya samar da birane masu kayatarwa wadanda ba za su kasance masu barazana ga mahalli ba.

Yanzu haka a China, mutane da dama sun fara mayar da hankali kan batutuwa da suka shafi canjin yanayi fiye da da kamar yadda rahotanni suka nuna.