Amurka ta jefa wa Kurdawa makamai

Syria Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Turkiya ta ce ba za ta taimakawa Kurdawa da makamai ba

Wasu Jiragen yakin kasar Amurka sun jefa makamai da kayayyakin agaji ga mayakan Kurdawan da ke kare garin Kobani a kan iyakar kasar Syria.

Kuradawn dai suna kare garin na Kobani ne daga yunkurin da mayakan IS masu da'awar kafa daular musulunci ke yi na kutsawa cikin garin.

Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon ta ce jiragen sun yi safarar kayayyaki ne da Kurdawan kasar Iraqi suka samar.

Sai dai a daya bangaren kasar Turkiya ta ce ba za ta taimakawa Kurdwan da makamai ba, duk da cewa garin na Kobani na kusa da iyakarta.

Turkiya dai na yiwa mayakan Kurdawan kallon kungiyar 'yan ta'adda ne, duk da cewa suna yaki da mayakan na IS.