'Shakku kan yarjejeniya da Boko Haram'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kawo yanzu Abubakar Shekau bai fitar da sanarwa ba kan batun tsagaita wuta da gwamnatin Nigeria ba

'Yan Nigeria da dama na ci gaba da nuna shakku kan batun yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ce an cimma tsakanin kungiyar Boko Haram da gwamnatin kasar.

Kwanaki biyu bayan shelar da gwamnatin kasar ta yi cewar ta soma sasantawa da Boko Haram, sai mayakan kungiyar suka kaddamar da hare-hare a wasu garuruwa da ke jihohin Borno da Adamawa.

Mazauna garin Abadam a jihar Borno da kuma al'ummar kauyen Gyarta a jihar Adamawa sun bayyana cewar mayakan Boko Haram sun farmusu a karshen mako inda suka hallaka mutane da dama.

Shi ma Malam Shehu Sani, shugaban kungiyar kare hakkin bil adama ta Civil Liberty Congress,ya ce akwai ayar tambaya game da ikirarin dakarun Nigeria kan batun tsagaita wuta da Boko Haram.

A halin yanzu dai 'yan Nigeria sun zaku su ji an yi sulhu da 'yan Boko Haram domin kawo karshen zubar da jini a cikin kasar.