Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram a Damboa

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Dakarun Nigeria na shan suka kan yaki da Boko Haram

Rahotanni daga garin Damboa na jihar Borno sun ce an kashe 'yan Boko Haram da dama a artabu tsakaninsu da jami'an tsaron Nigeria a ranar Lahadi da yamma.

Wani mazaunin garin Damboa ya shaidawa BBC cewar lamarin ya rutsa da 'yan Boko Haram da dama wadanda suka kaiwa garin hari amma kuma dakarun Nigeria suka samu galaba a kansu.

Hakan na faruwa ne duk da ikirarin tsagaita wuta da aka yi shellar cimma tsakanin sojojin Nigeria da kuma kungiyar ta Boko Haram.

Garin Damboa na daga cikin garuruwan da 'yan Boko Haram suke kaiwa hare-hare a jihar Borno inda suka kashe mutane da dama da kuma janyo hasarar rayuka.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane a Nigeria musamman a arewacin kasar.