Ghana: Akufo Addo zai tsaya takara

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan shi ne karo na uku da Akufo ke tsayawa takarr shugabancin kasar.

A kasar Ghana, a karo na uku babbar jam'iyar adawar kasar, NPP ta sake zaben Nana Akufo Addo a matsayin wanda zai yi mata takarar shugabancin kasar a zaben 2016.

Jam'iyar dai ta zabi Nana Akufo Addo ne a zaben fid-da gwanin da ta gudanar a dukkan sassan kasar a karshen makon jiya.

Ya lashe sama da kashi casa'in bisa dari na kuri'un da aka kada kuma ya doke wasu mutane biyu da suka yi takara da shi.

Mr Addo ya taka rawar gani a zaben shekarar 2010 wanda shugaba John Mahama ya lashe.

Karin bayani