Babu sauran cutar Ebola a Nigeria - WHO

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Gwamnatin Nigeria ta dauki matakan murkushe cutar a fadin kasar

Hukumar Lafiya ta Duniya-WHO ta ayyana kasar a matsayin wacce ta kawar da cutar.

Hakan na zuwa ne bayan da aka kwashe makonni shida ba a samu rahoton wani da ya kamu da cutar ba.

Sai dai masana harkokin lafiya sun ce cutar ka iya dawowa cikin kasar.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani taro da take yi da jami'an hukumar lafiya ta Nigeria a Abuja.

A watan Yulin da ya gabata an yi matukar damuw bayan wani jami'in diplomasiyyar Liberia ya shigo da cutar zuwa Nigeria - kasar da ke da cunkoson jama'a kusan miliyan 170.

Sai dai adadin mutanen da suka mutu ya ragu zuwa takwas, kuma kwararru sun ce irin yadda aka yi yaki da cutar a Nigeria darasi ne ga wasu kasashen duniya a kokarin dakile yaduwar cutar.

Karin bayani