An yi watsi da mu a Saudiyya - Alhazan Nijer

Shugaban Nijer Muhammadu Issofou Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Nijer Muhammadu Issofou

A Jamhuriyar Nijar, wasu alhazai da suka koma gida bayan kammala aikin Hajji, sun koka game da halin da suka gudanar da ayyukan hajin a cikinsa.

Alhazan, sun zargi kamfanonin hajjin da suka yi jigilarsu da ma hukumar ayyukan haji ta kasar ta Nijar, wato (COHO) da rashin kula da su a kasa mai tsarki.

Wasu Alhazan sun ce ba a ba su isasshen abinci ba kuma wuraren kwanciya ba su wadace su ba.

Wadanda suka yi koken, sun ce, ba su sanya jami'an hukumar Alhazan kasaar a ido ba don share musu hawaye.

Amma wasu kamfanonin aikin hajin sun musunta wannan zargin.

Karin bayani