Brittaniya na tara bayanan cin zarafin Yara

'Yan Sandan Brittaniya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan Sandan Brittaniya

Brittaniya za ta kirkiro wata cibiya ta kasa ta tattara hotunan batsa da lalata da kanana Yara wadanda aka kwace lokacinda 'yan sanda suka kai samame a shafukkan Internet na masu lalata kananan Yaran inda ake tallar hotunan.

Cibiyar tattara hotunan na lalata da kanana Yaran za ta taimaka ma 'yan sandan Brittaniya hada gwiwa wajen bincike a kan lalata da kanana Yara.

Karuwar hotunan lalata da kananan yaran a Internet yana nufin ana bukatar karin taimako wajen tantance abinda aka kwace.

Cibiyar tara bayanan wani bangare ne na namijin kokarin da kasashen duniya ke yi na tsara hotunan da kuma bin sawun wadanda ke da hannu a lamarin.

Bukatar kafa cibiyar ta taso ne saboda daukar irin wannan matakin a kan wadanda suka ci zarafin kananan yaran da shafukan internet yawanci suna barin 'yan sanda ne da bukatar tsara daruruwan dubban hotunan, a wasu lokutta ma miliyoyi.

Yawancin wadannan hotunan an ganzu a wasu lokutta saboda tallar su da ake yi ta sa an buga su, an kuma kara buga su a wasu wuraren a lokutta da dama. Wannan zai sanya masu binciken su gaza wajen bin diddigin wadansu wadanda ba a gani ba.

A cikin wata sanarwa Minista mai kula da harkokin 'yan sanda Mike Pinning ya ce "Cibiyar tattara bayanai game da lalata da kananan yaran wani babban yunkuri ne a yanzu a kokarin da gwamnati ke yi na kawo karshen miyagun laifukkan da ake tafka ta internet ta ci da gumin kananan yara."

Yace, "sakamakon shi zai haifar da canjin rayuwa, wannan shine muhimmancin dake tattare da wannan Cibiya."

Har ila yau kuma Cibiyar tattara banana, wani bangare ne na kokarin da kasashen duniya ke yi a wani tsarin da ake kira "project Vic" wanda ke kokarin tsara hotunan da jami'an tsaro suka kame a sassa dabam-dabam na duniya.

Richard Brown daga Cibiyar Yaran da suka bace da wadanda ake ci da guminsu, wadda ke taimakawa wajen tafiyar da aikin Projecy Vic, ya ce wasu tsare-tsaren biyu da aka kirkiro suna amfani da wannan hanyar don tabbatar da cewa, za a iya gane hotunan da aka dauka a lokutta da dama.

Karin bayani