Mayakan IS na iya fuskantar zargin laifukkan yaki

Mayakan IS . Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan IS .

Shugaban hukumar kare hakkin bil'adama a Majalisar Dinkin Duniya ya ce mayakan Islama na IS za a iya samunsu da laifin yaki da yunkurin kisan kare dangi.

Ivan Simonovic, wanda ya dawo daga ziyarar mako guda ta gani da ido kasar Iraqi, ya ce a wajen mayakan Islamar adalci shi ne kisa.

Ya kuma zarge su da aikata ayyukan keta hakkin bil'adama da suka hada da sayar da 'yammata don yin lalata da su.

Mr Simonovic ya ce matakin da suka dauka kan 'yan kabilar Yazidi tsiraru yunkuri ne na aikata kisan kare dangi, domin ba su da wani zabi da ya wuce ko dai su karbi addinin musulunci ko kuma mayakan IS su hallaka su.