An yanke wa Pistorius daurin shekara biyar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kotun ta yi wa Pistorius daurin-talala saboda mallakar makami

Kotu a Africa ta Kudu ta yanke wa dan tseren nan, Oscar Pistorius, hukuncin daurin shekara biyar bayan da ta same shi da laifin kisan burdurwarsa, Reeva Steenkamp, ba da gangan ba.

Sai dai kotun ta wanke shi daga zargin cewa ya yi kisan ne da gangan.

Mai shari'a, Thokozile Masipa, ta same shi da laifin kisa ba da gangan ba, lokacin da ya harbi Miss Steenkamp a cikin makewayin gidansa a Pretoria.

Har ila yau, an yanke masa hukuncin daurin shekaru uku na je-ka-gyara halinka bisa laifin saba ka'idar amfani da bindiga.

Lauyan mai shigar da kara ya bukaci mai shari'ar ta yanke wa Pistorius hukuncin akalla shekaru goma a gidan yari bisa wannan kisan.

Bisa wannan hukuncin dai, dole ne Mr Pistorius ya shafe watanni takwas a gida yari kafin a ba shi damar soma walwala.

Iyalan Ms Steenkamp dai sun yi murna da wannan hukunci.

Karin bayani