Likitoci suna yajin aiki a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Likitocin na yajin aikin ne lokacin da 'yan kasar ke fama da matukar zazzabin cizon sauro

A jamhuriyar Nijar, kananan likitocin karkara sun fara yajin aiki na kwanaki uku a fadin kasar baki daya.

Likitocin suna neman gwamnati ta biya musu wasu bukatoci ne da suka hada da daukarsu aiki dindindin da mayar da albashinsu karkashin ministan kiyon lafiya da dai sauransu.

Wakiliyar BBC a Nijar da ta ziyarci wasu yankunan karkarar ta ce yajin aikin ya yi tasiri ganin cewa 'yan kasar na fama da matukar zazzabin cizon sauro a wannan lokaci.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da likitoci a kasar ke tsunduma cikin yajin aiki ba.

Karin bayani