al-Bashir zai sake yin takara a Sudan

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Jam'iyyar ta ce sunan al-Bashir kadai za ta mika don yi mata takara

Jam'iyyar da ke mulkin kasar Sudanta sake zabar shugaba Omar al-Bashir domin ya tsaya takara a karkashinta a zaben da za a yi a badi.

Za a yi zaben ne a watan Aprilu.

Jami'iyyar mai suna The National Congress Party ta ce sunan shugaba al-Bashir kadai za ta mika domin a amince da shi a taron da za a yi domin tsayar da dan takara ranar Alhamis.

Kotun duniya dai tana neman al-Bashir ruwa-a-jallo saboda zargin da take yi masa na aikata kisan kare-dangi da laifukan yaki a yankin Darfur.

al-Bashir ya sha musanta zargin.

Karin bayani