Za a hana amfani da maganin kwari a Turai

Britain Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hana yin amfani da magann kwarin zai taimaka wajen kare muhalli

Matakin da kungiyar tarayyar turai ta dauka na hana yin amfani da maganin kwari, zai iya shafar hatsin da ake nomawa a Burtaniya, wani rahoto ya bayyana.

Har ila yau rahoton wanda wasu kungiyoyin manona uku suka fitar ya kuma nuna cewa hana yin amfani da maganin kashe kwari a gonakin Burtaniya zai iya sa farashin kayan masarufi su yi tashin goron zabi.

Rahoton ya kuma kara da cewa hakan zai shafi ribar da manona ke samu matuka.

Nan da shekarar 2020 ne kungiyar tarayyar ta turai ta ke shirin hana yin amfani da wasu sinadirai guda 40 domin a rage illar da suke haifarwa ga muhalli.

Baya ga matsalolin da rahoton ya bayyana a baya akwai karin kwari da za a samu a gonaki wadanda za su yi illa ga noman kayan abinci irinsu dankali da karas da wake da dai sauransu.

Kungiyoyin masu ra'ayin mazan jiya dai sun yi maraba da wannan shiri na hana yin amfani da sinadaran duk da irin matsalolin da hakan ka iya haifarwa.

A dai shekarar 2009, majalisar dokokin kungiyar tarayyar turai ta amince a rage yawan maganin kwari da ake amfani da su a gonaki a nahiyar.

A lokacin an hana yin amfani da ire-ire wadannan maganin kwari guda 22 domin ana ganin za su iya haifar da matsalar sankara a jikin dan adam.