Ebola: Ana tsangwamar bakaken fata a Amurka

Ebola
Image caption Ana nuna kyama ga bakaken fata 'yan asalin Afrika a wasu wurare a Amurka

Bakaken fata a Amurka sun koka da yadda ake tsangwamarsu tun bayan da aka samu barkewar cutar Ebola.

Lamarin yayi kamari ne tun bayan mutuwar dan kasar Liberiyan nan Thomas Eric Duncan a birnin Dallas da ke jihar Texas a Amurka a ranar 8 ga watan Oktoba, bayan ya kamu da cutar ta Ebola, ta sa ana ci gaba da tsangwamar 'yan kasashen Afrika da ke zaune a Amurkan.

Wakiliyar BBC Leslie Goffe dake birnin New York ta ruwaito cewa lamarin ya kai ga har ana haramtawa wasu 'yan Afrika zuwa wuraren aiki tare da kyamar su a wasu wurare da jama'a kan taru.

Cutar ta Ebola yanzu haka ta kashe mutane sama da dubu 4500 a tsakanin kasashen Liberiya da Guinea da Saliyo da ma Nijeriya wacce ta shawo kan cutar nan ba da jimawa ba.