'Da 'yan Boko Haram na ainihi muka gana'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kawo yanzu Abubakar Shekau bai ce komai ba kan yarjejeniyar

Gwamnatin Nigeria ta ce tana nan kan bakarta cewa wadanda ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da su 'yan kungiyar Boko Haram ne na ainihin.

Jama'a da dama a kasar sun shiga nuna shakku kan sahihancin bayanan da gwamnatin ta bayar saboda yadda aka ci gaba da kai hare-haren tun bayan sanar cimma yarjejeniyar.

A wata kebantacciyar hira da ya yi da BBC, karamin ministan harkokin wajen kasar wanda kuma shi ne minista mai kula da ma'aikatar watsa labarai Dr. Nurudden Muhammad ya ce gwamnatin na da yakini sosai kan cewa wadanda ta tattauna da su a birnin Njamena na kasar Chadi mayakan Boko Haram ne.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane musamman a wannan shekarar a arewacin Nigeria.