Ebola: Nigeria za ta tura likitoci 600 Africa ta yamma

Image caption Hukumar lafiya ta ayyana Nigeria a matsayin kasar da ta yi nasarar kawar da ebola

Gwamnatin Nigeria ta ce ta horar da likitoci da ma'aikatan lafiya dari shida kan yaki da Ebola domin taimaka wa kasashen Afrika ta yamma da ke fama da cutar.

Ministan lafiya na kasar, Dokta Khaliru Alhassan ya shaida wa BBC cewa an raba likitocin gida biyu: kashi daya za su zauna a Nigeria domin tunkarar cutar idan ta sake barkewa, daya rabin za a tura su kasashen da ke fama da cutar domin bayar da gudunmawarsu.

Ya kara da cewa tun lokacin da cutar ta Ebola ta kunno kai a yankin Africa ta yamma, Nigeria ta sha alwashin taimaka musu da ma'aikatan lafiya da za su kai musu dauki.

A ranar Litinin ne Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana Nigeria a matsayin wacce ta yi nasarar kakkabe cutar kwata-kwata, kodayake ta yi gargadin cewa kasar na cikin hatsarin sake samun cutar in har akwai ta a sauran kasashen yankin na yammacin Africa.

Karin bayani