Ebola - Ana tsangwamar wadanda suka yi jiyya

Likitocin Ebola a Nijeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Likitocin Ebola a Nijeriya

Bayan da hukumar lafiya ta duniya ta ayyana Najeriya a zaman wadda ba ta yi nasarar kakkabe cutar Ebola...

wadanda suka tsira da rayukkansu daga cutar bayan da suka kamu da ita, sun ce babban aikin da ke gaban hukumomin kasar a yanzu shi ne daukar matakan hana nuna musu kyama da sauran jama'ar kasar ke yi.

A yayin da ta ke Magana gaban taron da aka yi domin ayyana Najeriya a matsayin kasar da ta kawar da cutar, daya daga cikin wadanda suka samu warkewa, ta shaida wa jami'an Najeriya cewa a halin da ake ciki, ita da 'yan uwanta suna fuskantar tsangwama.

Karin bayani