An kafa rundunar hana satan shanu a Najeriya

Rustling
Image caption Za a kafa rundunar a duk shiyoyin Najeriya guda shida

A Najeriya, babban Sifeton 'yan sandan kasar Suleiman Abba, ya bada sanarwar kafa runduna ta musamman domin yaki da matsalar sace sacen shanu da ake yi a kasar.

A wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan kasar Emmanuel Ojukwu ya aikewa da BBC ya ce za'a kafa rundunar a shiyoyin kasar guda shida, kuma za su kasance ne karkashin jagorancin mataimakin sifeton 'yan sandan kasar.

Alhaji Bello Bodejo, shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore, ya ce wannan abin farin ciki ne domin zai taimakawa Nijeriya wajen bunkasar tattalin arzikinta.

Matsalar satar shanu a Nijeriya ya zama ruwan dare a kasar inda a lokuta da dama ya kan haifar da rikici tsakanin kabilu.