Majalisar Rwanda ta haramta BBC a kasar

rwanda da bbc

Majalisar dokokin Rwanda ta kada kuri'ar haramta BBC a kasar sakamakon wani shirin talabijin game da kisan kare dangi a kasar a 1994.

Shirin BBCn na wannan duniya, Labarin da ba a fada ba game da Rwanda, wanda aka watsa a farkon watan nan, ya nuna shakku game da wasu bayanan gwamnati kan abin da ya faru a lokacin kisan kare dangin.

Wakilan majalisar sun kada kuri'a don baiwa gwamnati shawarar cewar a gurfanar da 'yan jaridar da suka hada shirin.

Tun farko mutane kusan dari da hamsin sun yi zanga zanga a wajen Ofishin BBC a Kigali babban birnin Rwanda.