"Fom din APC ya yi tsada da yawa"

Image caption 'Yan jam'iyyar APC sun ce za su bukaci a rage kudin sayen fom

Wasu mutane da ke son yin takara a karkashin jam'iyyar APC a Nigeria sun ce an tsawwala kudin sayen fom din yin takara.

Masu son yin takarar sun ce jam'iyyar ta yi hakan ne domin ta share wa 'yan-jari-hujja fage don yin takarar a karkashinta, sabanin ikirarin da take yi cewa za ta kawo sauyi a siyasar kasar.

Malam Muhyi Magaji ya shaida wa BBC cewa za su yi bakin kokarinsu wajen ganin jam'iyyar ta rage kudin sayen fom din.

Sai dai jam'iyyar ta ce fom din bai yi tsada ba domin da kudin fom din take amfani wajen gudanar da aikace-aikacenta.

A baya dai, Janar Muhammadu Buhari, daya daga cikin masu son yi wa jam'iyyar takarar shugabancin kasar, ya koka kan yadda aka tsawwala kudin sayen fom din.

Karin bayani