Kokwanto a kan sakin 'yanmatan Chibok

'yan matan chibok Hakkin mallakar hoto AP

Gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu ba su cimma matsaya ba kan ranar da za a sako 'yan matan Sakandaren Chibok da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace ba.

A makon jiya ne dai mahukuntan kasar suka bayyana fatan cewa watakila za a sako 'yan matan a wannan makon, bayan sun ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta, kamar yadda suka yi ikirari.

Lamarin dai ya sa iyaye da wasu masu fafutuka sun hallara a dandalin Unity Fountain da ke birnin Abuja suna dakon zuwan 'yan matan, a ranar Litinin din da ta gabata.

Amma a hira da yau din nan, shugaban cibiyar samar da bayanai a kan yaki da ta'addanci a Najeriya, Mr. Mike Omerim ya ce da ma can gwamnati ba ta sanar da rana takamaimai ba da za a sako 'yan matan.

A madadin haka, ‘yan bindiga sun sake sace wasu matan ne da kananan yara fiye sittin a jihar Adamawa ta Najeriyar.