Gwamnati na yin kafar-ungulu a takara ta- Kwankwaso

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kwankwaso ya ce ba zai fasa ayyana takararsa ba.

Gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayyar Nigeria da kin ba shi filin da zai yi shelar takararsa ta shugaban kasa.

Gwamnan ya ce ya aike da wasika ta neman amincewa daga gwamnati domin ya yi amfani da filin Eagles Square da babban dakin taro na International Conference Centre amma an ki amince masa.

A cewar gwamnan, yanzu abin da ya rage masa shi ne ya hau kan titunan Abuja ranar 28 ga wannan watan domin bayyana aniyar takararsa a karkashin jam'iyyar APC.

A baya dai wani mai neman takara a jam'iyyar Janar Muhammadu Buhari ya yi amfani da Eagles Square ne domin yin shelar takarasa a karkashin jam'iyyar APCn.

Gwamnatin tarayya, karkashin jagorancin shugaba Goodluck Jonathan ba ta ga-maciji tsakaninta da gwamna Kwankwaso saboda sukar da yake yi mata tun bayan komawarsa jam'iyyar APC daga jami'iyyar PDP mai mulki.

Karin bayani