Microsoft zai yi fatali da sunan Nokia akan wayoyinsa

Hakkin mallakar hoto AFP

Kamfanin Microsoft zai yi fatali da samfurin sunan Nokia daga sabbin wayoyinsa na tafi da gidanka.

Hakan na zuwa kasa da shekara guda bayan kamfanin na Microsoft ya mallaki wani bangare na kamfanin Nokia.

Kamfanin ya ce a yanzu za'a rinka kiran sabbin wayoyin Nokia Lumia da sunan Microsoft Lumia

Sauran bangarorin Nokia da Microsoft bai saya ba, za su ci gaba da amfani da sunan.

Kamfanin Microsof ya sayi wani bangare na Nokia ne a watan Afrilu akan kudi $7.2bn

Kuma tun daga wancan lokacin, sannu a hankali microsoft ya janye kansa daga samfurin wayar Nokiar

Kamfanin ne ya tabbatar da janyewar a shafinsa na facebook da yake amfani da shi wajen tallata wayoyin na harshen faransanchi.

Sai dai sanarwar bata hana kamfanin Microsoft daga cigaba da amfani da samfurin sunan Nokiar ba akan wasu wayoyin sa marasa karfi, wanda kamfanin yake da hakkin kerawa har kusan shekaru goma.

A yanzu dai kamfanin Microsoft na gudanar da garanbawul.

A watan Yuli, babban jami'in kamfanin Satya Nadella ya bada sanarwar zaftare guraben ayyuka 18,000.

Galibin guraben ayyukan da aka zaftare, kusan 12,500 zasu kasance ne daga ma'aikatan da aka dauka bayan mallakar Nokia.