An daure mata hudu a Saudi Arabia

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An samu matan ne da laifin goyon bayan al-Qaeda

An yanke wa wasu mata hudu hukuncin zaman kurkuku a Saudi Arabia bayan an kama su da laifin tallafa wa kungiyar Al Qaeda, ciki har da barin 'ya'yansu su zama masu jihadi.

Kafar watsa labaran gwamnatin kasar ta bayyana cewa za a daure matan ne daga shekara shida zuwa shekara goma.

Kazalika an kama su da laifin amfani da shafukan intanet din da aka toshe, inda suka wallafa hotunan da ke nuna yadda ake yin gwagwarmaya.

Mahukunta a kasar ta Saudi Arabia sun kaddamar da dokoki masu tsauri a shekarar da ta gabata domin hana 'yan kasar shiga kungiyoyin masu jihadi.

Masu kare hakkin dan adam sun ce matakin ya hada da mutanen da suke furta kalamai kan harkokin siyasa da na yau-da-kullum a intanet.

Karin bayani