An sace kanwar Diezani Madueke

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mrs Madueke na da karfin fada a ji a gwamnatin Jonathan

'Yan sanda a jihar Ribas sun tabbatar da sace kanwar ministar man fetur ta Nigeria mai karfin fada a ji, Mrs Diezani Alison-Madueke.

An ambato, kakakin rundunar 'yan sanda jihar Ribas, Ahmad Muhammad na cewar 'yan bindiga sun yi awon gaba da Osio Agama a ranar Talata a birnin Fatakwal.

Kakakin 'yan sandan ya ce kawo yanzu ba suda bayani ko 'yan bindigar sun nemi a biya kudin fansa ko kuma a'a.

Sace mutane domin kudin fansa babbar sana'a ce a yankin kudu maso kudancin Nigeria.

A lokutan baya an taba sace mahaifiyar ministar kudin Nigeria, Dr Ngozi Okonko-Iweala da kuma kawun Shugaba Jonathan a jihar Bayelsa.