Ebola: Yarinyar da ta kamu da cutar a Mali ta rasu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Samun dukkanin mutanen da suka hadu da yarinyar shi ne babban kalubale ga gwamnatin Mali

Yarinyar nan mai shekaru biyu da haihuwa wacce aka tabbatar da cewa ita ce mutum ta farko da ta kamu da cutar Ebola a Mali ta rasu.

Hukumar Lafiya ta duniya (WHO) ta kuma ce yarinyar ta yi tafiyar daruruwan kilomita a motar safa a cikin kasar, dauke da alamomin cutar.

An dai kebe mutane fiye da 40 din da suka hadu da yarinyar.

Kakarta ce ta kai ta Mali bayan jana'izar mahaifiyarta a Guinea, daya daga cikin kasashen da cutar tafi muni.