Ana zaman makoki a Masar

Hakkin mallakar hoto

Hukumomi a Kasar Masar sun ayyana makokin kwanaki uku bayan rundunar sojin Kasar ta yi asarar sojojinta akalla 31.

Wannan shine asarar rayuka mafi girma da dakarun Masar suka fuskanta cikin shekaru da dama a kasar

An dai kashe akalla sojoji 31 a wasu hare- hare guda biyu da aka kai wurin duba ababan hawa

An kuma sanya dokar ta baci a wasu wurare dake yankin Sinai inda aka kai harin

Bayan takaita zirga zirga, za kuma a rufe kan iyakar Masar da kuma zirin Gaza

Wakiliyar BBC ke nan take cewa Hare- haren da mayakan Jihadi suke kaiwa jami'an tsaron Masar a yankin Sinai ya karu ainun, tun lokacin da sojoji suka hanbarar da shugaba Mohammed Morsi a bara