Gwamna zai yi murabus saboda sace dalibai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Angel Aguirre yana fuskantar suka daga 'yan kasar

Gwamnan jihar Guerrero da ke Mexico ya ce zai yi murabus saboda har yanzu ba a gano dalibai 43 da suka bata fiye da wata daya da ya wuce ba.

Gwamnan, mai suna Angel Aguirre ya sha suka daga 'yan kasar da ma kiraye-kirayen ya sauka daga mulki tun bayan batan daliban lokacin da aka yi arangama da 'yan sanda a birnin Iguala.

Babban mai shari'a na kasar ya ce da alama akwai alaka ta kut da kut tsakanin 'yan siyasa da 'yan sanda da kuma masu safarar miyagun kwayoyi a jihar ta Guerrero.

Ya kara da cewa gwamnan na Iguala, wanda ya tsere, shi ne ya bukaci 'yan sanda su kama daliban sannan suka mika su ga 'yan daba.

Karin bayani