Mata za su fara yajin jima'i a Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu fafutikar sun ce yajin yin jima'i zai iya magance yakin da ake yi

Mata masu fafutika a Sudan ta Kudu sun bai wa matan kasar shawara su ki amincewa idan mazansu sun nemi kwanciya da su har sai sun kawo karshen yakin basasar da ake yi.

A cewar jaridar Sudan Tribune da ake wallafawa a kasar, masu fafutikar suna so matan su yi hakan ne domin karfafa wa mazan gwiwa don su sasanta da juna.

An kawo wannan shawara ne a lokacin da masu fafutikar su 90, cikinsu har da 'yan majalisar dokoki, suka gudanar da wani taro a Juba, babban birnin kasar.

A wata sanarwa da suka fitar sun ce, "Babbar shawarar da muka bayar ita ce, a wayarwa mata kai domin su ki kwanciya da mazansu har sai sun samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu."

Karin bayani