Ana cin zarafin manyan mutane ta intanet

Hakkin mallakar hoto think stock
Image caption An fi cin zarafin maza ta hanyar kiran su da sunayen banza, mata kuwa, kalaman lalata ake musu

Wani rahoto da wata cibiyar binciken al'amuran intanet a Amurka ta fitar, ya nuna cewa kimanin kashi arba'in cikin dari na manyan mutane da ke amfani da intanet a kasar sun fuskanci cinzarafi.

Binciken ya nuna cewa cinzarafi ta hanyar kiran mutane da sunayen banza da yi musu barazana, abu ne da a ke yawan faruwa a intanet.

Rahoton binciken ya nuna cewa anfi kiran maza da sunayen banza, yayin da mata kuwa su kafi fuskantar kalaman lalata.

Sakamakon binciken ya zo ne a daidai lokacin da a ke yawan samun matsaloli cin zarafi a shafukan sada zumunci na intanet musanman ga mata masu sharhi a kan wasannin kwamfuta.

A cewar rahoton, mutane da ke tsakanin shekaru 18 zuwa 29 su suka fi zama cikin hadarin cin zarafi ta intanet, inda kashi 65 cikin dari na masu amfani da intanet daga cikin su suka ce, sun taba fuskantar matsalar.

Binciken ya gano cewa an fi samun matsalar cin zarafin ne a shafukan sada zumunci na intanet.

Abubuwa shida binciken ya maida hankali a kai; kiran mutane da sunayen banza, da yunkurin cin zarafin mutane da gangan, da lokacin da a ke dauka a na cin zarafin mutane, da barazana, da bibiya, da kuma kalaman lalata.

Mawallafin rahoton, Maeve Duggan ta ce "a kwai abin mamaki yadda a ke samun nau'o'in cin zarafi daban daban ta hanyoyi daban daban a intanet".

Binciken ya nuna cewa akasarin mutanen da a kaci zarafinsu a intanet suna barin abin ya tafi a haka.

A cikin makon da ya gabata, fiye da mutane dubu biyu ne suka sa hannu a wata wasika ta kowa da kowa, inda su ka yi kiran a kawo karshen tsana da maganganun cin zarafi a shafin Twitter da sauran shafukan sada zumunci, bayan an aikawa Anita Sarkeesian, wadda tayi sharhi akan wasu wasannin kwamfuta, sakonnin barazanar kisa.