Daruruwan 'yan hijira a tsaunin Cirji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijira a Najeriya

A Najeriya, wasu daruruwan mutanen kauyen Kamale a Karamar Hukumar Michika ta jihar Adamawa wadanda ke gudun hijira a saman tsaunin Cirji a iyakar kasar da Kamaru sun koka da mawuyacin hali da su ke ciki.

Rahotanni sun ce mutanen sun shafe kimanin makonni biyu suna saman tsaunin ba abinci da katifun kwanciya.

Sai dai Hukumomi a Najeriyar sun ce basu san da mutanen a saman tsaunin Cirjin ba, shi yasa ba a kai musu tallafi ba.

Hukumar bada agajin gaggawa a Najeriya-NEMA ta ce ta na shirye shiryen kai dauki ga mutanen da ma wasu 'yan kasar da ke gudun hijira a Kamaru.

Hukumar ta NEMA ta ce kimanin mutane dubu- dari- bakwai da hamsin ne rikice-rikice da sauran bala'o'i suka raba da muhallansu a sassa daban-daban na kasar.