'Sojin hadin-gwiwa sun kwato Abadam'

Hakkin mallakar hoto reuters

Rahotanni daga Najeriya sun ce sojojin rundunar hadin-gwiwa ta kasa-da-kasa sun kwato garin Abadam na jihar Borno daga hannun 'yan Boko Haram.

Shaidu da majiyoyin tsaro sun ce sojojin sun kashe mayakan Boko Haram din da dama a musayar wutar da suka yi a tsakanin ranakun Juma'a da Asabar kafin kwace ikon garin, wanda ya fada hannun mayakan a makon jiya.

Wani dan garin Abadam din ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa sauran 'yan Boko Haram din sun tsere, kuma jama'a har sun fara komawa gida.

Sai dai ya ce "matsalar ita ce har yanzu jami'an tsaron ba su je suka zauna a garin ba". Bayan dai da suka kori 'yan Boko Haram din sun tafiyarsu, inji shi.

Haka kuma akwai matsalar rashin abinci a garin. Ya ce: "Abinci babu duk 'yan Boko Haram sun sace."

Hukumomi a Najeriya dai ba su yi wani bayani ga jama'a ba akan lamarin.

Lokacin da 'yan Boko Haram suka kwace Abadam din a makon jiya yawancin mutane garin sun tsere ne zuwa Jamhuriyar Nijer, wasu kuma suka ruga zuwa wasu sassa na Najeriya.

Karin bayani