'An kashe 'yan Boko Haram 39 a Kamaru'

Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumomi a Jamhuriyar Kamaru sun ce mayakan kungiyar Boko Haram daga Najeriya kusan 40 ne aka kashe a arewa maso gabashin kasar.

Ma'aikatar tsaro ta kasar Kamarun ta ce dakarunsu sun fafata da mayakan masu dauke da manyan makamai da suka tsallaka daga Najeriya suka kaiwa kauyuka ukku farmaki.

Fararen hula hudu ne aka ce sun halaka, amma babu wasu bayanai da suka nuna wadanda suka mutu ko suka samu raunuka daga bangaren dakarun na Kamaru.

A watannin baya bayan nan kungiyar ta Boko Haram ta fara kutsawa cikin kasar ta Kamaru, inda a wasu lokuttan ta kan sace da kuma yi garkuwa da mutane.

A waje daya kuma, rahotanni sun nuna cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a garin Gouye da ke kusa da Fotokol, a iyakan Kamaru da Najeriya, inda tarin 'yan gudun hijira suke zaune.

Harin ya biyo bayan ziyarar da manyan hafsoshin soja na Kamaru suka kai ta daukacin iyakokin Kamaru da Najeriyar a lardin arewa mai nisa domin jinjina wa dakarunsu.

Biyu daga cikin 'yan gudun hijirar sun gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa an samu asarar rayukan jama'a a wannan harin -- lamarin da ya kara tada hankalin jama'a.

Karin bayani