Ebola: Ma'aikaciyar Jinya ta fuskanci tsangwama

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amurkawa na daukar matakin kariya daga cutar

Ma'aikaciyar Jinyar nan wacce aka killace domin a gwada lafiyarta , bayan ta koma Amurka daga Saliyo, ta soki yadda hukumomi sukai mata.

Wasu sabbin ka'idoji da wasu jahohi uku na Amurkar suka bullo da su, sun ce wajibi ne a killace duk mutumin daya fito daga wata kasa a Yammacin Afirka da cutar ebola ta bulla , har tsawon kwanaki 21.

Casey Hick Ox, tace abinda akai mata nada- ban- tsoro, kuma tace hakan zai iya karyawa sauran ma'aikatan lafiya gwiwar tafiya zuwa Yammacin Afirkar domin taimakawa masu fama da cutar Ebolan.

Wakilin BBC yace sai da aka dauki sa'oi 4 ana mata tambayoyi, sannan aka ce mata jikinta yayi zafi saboda fargabar data samu kanta ciki.

Daga baya motocin 'yan sanda guda 8 tare da jiniya ne sukai mata rakiya zuwa asibiti, inda gwaji kuma ya nuna cewa bata dauke da kwayar cutar ebolan