Google ya bullo da manhajar "Inbox"

Hakkin mallakar hoto GOOGLE
Image caption Manhajar "Inbox" ta na janyo hankali a kan muhimman sakonni

Kamfanin Google ya na farfado da tsarinsa na aikawa da sakon Email, inda ya bullo da sabuwar manhajar wayar salula ta aika wa da sakonnin email da ake kira "Inbox".

Wannan wani yunkuri ne na sake fasalin akwatunan karban sakonnin na Email, da tabbatar da mutane ba su kuskure muhimman sakonni ba.

A yanzu haka kamfanin na Google ya gayyaci wasu masu amfani da hanyar aikawa da sakonni ta Gmail da su gwada aiki da sabon tsarin.

Wasu kwararru sun yi amanna sabon tsarin na Inbox zai maye gurbin Gmail.

Daya daga cikin shugabannin Google ya ce ''daya daga cikin manyan sauye-sauyen da muka yi tunda muka fara Gmail, shi ne Inbox, kuma tsari ne mai kayatarwa''.

Cikin sauye sauyen da sabon tsarin zai kunsa sun hada; janyo hankali a kan muhimman sakonni, kamar bayanai a kan tikitin jirgi, da hotuna da kuma sha'ani.

Sabon tsarin zai bai wa masu amfani da shi damar seta lokacin tunatar da su yin wasu muhimman abubuwa.