Likita zata kai karar jami'ai a Amurka

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Fadar White House ta ce bata amince da killace mutane na dole ba

Wata ma'aikaciyar Jinya da aka kebe a Amurka saboda fargabar Ebola ta ce zata kalubalanci killacetan da aka yi, a wata Kotun Gwamnatin Tarayya.

Lawyan Kaci Hickox yace abinda ta fuskanta ya tada wasu batutuwa muhimmai da suka shafi tsarin mulki da kuma 'yanci, ganin cewa ba a same ta da cutar ba bayan an yi mata gwaji.

Gwamnan birnin New York a yanzu ya sanar da cewa za'a baiwa mutum damar zuwa gidansa, domin asa-masa ido acan, a madadin a ajiye shi a inda gwamnati ta tanadar.

Tunda farko dai Fadar gwamnatin Amurka ta fadawa gwamnonin Jahohin New York da New Jersey da Ilinoy cewa, bata amince da matakin wajbata killace duk mutumin da ya fito daga kasar da ke fama da cutar Ebola har tsawon kwanaki 21.