Niger ta janye "kundin koyar da batsa"

Image caption Gwamnati ta janye manhajar ne bayan ta sha suka daga wurin malaman musulinci

Gwamnatin Jamhuriyyar Niger ta janye wata manhaja da take son kaddamarwa a makarantu domin barin dalibai su rika sumbatar juna.

Gwamnati ta dauki matakin ne bayan malaman addinin musulincin kasar sun ce manhajar za ta bata tarbiyyyar dalibai musulmai.

Kasar dai tana goyon bayan masu auren jinsi guda.

Akasarin 'yan kasar dai musulmai ne, kuma Niger tana cikin kasashen da aka fi yawan haihuwa a duniya.

Karin bayani