2015: Obasanjo ya gargadi PDP da APC

Hakkin mallakar hoto
Image caption Cif Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban Nigeria, Olusegun Obasanjo, ya gargadi manyan jam'iyyun kasar su yi la'akari da batun addinni wajen fitar da 'yan takararsu a zaben 2015.

A wata sanarwa, tsohon shugaban ya bukaci jam'iyyar PDP da kuma APC ka da su tsayar da mabiya addinni daya a matsayin dan takarar shugaban kasa da na mataimaki a zaben da ke tafe.

A cewarsa, lamarin zai kasance babu adalci, a tsayar da musulmi da musulmi ko Kirista da Kirista a matsayin 'yan takarar wata jam'iyyar a 2015.

Batun addinni na matukar tasiri a siyasar Nigeria musamman sakamakon irin rikici mai nasaba da addinni da kabilanci da ake fama da shi a wasu sassan kasar.

A cikin Fabarairun 2015 ne za a gudanar da zabuka a Nigeria lamarin da wasu ke ganin sai an yi takatsatsan saboda gudun tashin hankali.