An harbe kyaptin din Afirka ta Kudu har lahira

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutuwarsa za ta girgiza sauran abokan wasansa

An harbe har lahira Kyaptin din kungiyar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu Senzo Meyiwa.

'Yan sanda sunce an harbe mai tsaron gidan dan shekaru 27 a lokacin da wasu mutane suka kutsa kai gidan da yake ciki, a wani gari dake da nisan kusan kilomita 20 da kudancin birnin Johanesburg.

Wani wanda yai magana akan abinda ya auku, ya ce mutane bakwai ne suka kutsa kai cikin gidan, kuma daya daga cikinsu ya nemi golan ya bashi wayarsa, abinda yasa wata gaddama ta kaure tsakaninsu.

Kuma an bayyana rasuwar Golan bayan an kwantar da shi a asibiti.